Asalin hoton, Getty Images
Lamine Yamal ba zai bugawa Spain wasanta na gaba da za ta fafata da Serbia ba a ranar Talata sakamakon raunin da ya ji.
Dan wasan Barcelona ya ji raunin ne a ranar Asabar a wasan da suka yi nasara kan Denmark da ci 1-0.
A ranar Lahadi ne aka gwada mai shekara 17 aka tabbatar ya ji rauni, sannan Spain ta cire sunan ɗan wasan daga tawagarta.
“Gwajin da aka yi masa bai nuna takamaiman abin da ke damunsa ba, amma dai matsalar a cikin naman ƙafarsa ne kamar yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Spain ta bayyana.
“Saboda bai wa lafiyar ɗan wasan muhimmanci da kuma kare aukuwar wani raunin shi yasa aka cire sunansa daga tawagarmu,” in ji De la Fuente.
Tuni aka maye gurbin ɗan wasan da Rodrigo Riquelme na Atletico Madrid.
